Opens in a new window
Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta zama mafi ƙarfi a duniya
10 July 2026

Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta zama mafi ƙarfi a duniya

Bakonmu a Yau

About

Cikin makon nan, kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya, ta kafa tarihin zama mafi ƙarfi gami da bunƙasa a faɗin Duniya, bayan zarta mai riƙe da kambun a baya bayan nan, wato takwararta ta Korea ta Kudu.

 

Rahoton kamfanin Bloomberg ya nuna cewa, zuwa yanzu Kasuwar ta Najeriya ta samu tagomashi ne da kaso 67 cikin 100, yayin da ta Korea ta Kudu ke da kaso 66.

Domin jin ƙarin bayanin kan dalilan samun wannan nasara, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Ƙasim Garba Kurfi, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a kasuwar hada-hadar hannayen jarin ta Najeriya.

Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawar...