
About
A tsakiyar wannan mako, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shelanta kafa dokar ta ɓaci kan sha’anin tsaro a faɗin ƙasar, matakin da a ƙarƙashi ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin jami’an Ƴansanda dubu 50,000 domin murƙushe matsalolin tsaron da ke ta’azzara.
Kan wannan, da wasu ƙarin matakai da ake shirin ɗauka a ƙarƙashin dokar ta ɓacin kan tsaro Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhd Sani Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Tarayyar Najeriyar.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...