Kaftin Bakoji kan banbancin kudanci da arewacin Najeriya wajen tunkarar matsalar tsaro
Bakonmu a Yau
Wata matsala da masana tsaro ke tsokaci a kai a Najeriya, shi ne yadda ake samun banbanci tsakanin jihohin Arewacin ƙasar da na kudanci wurin tunkarar ƙalubalen tsaro a yayin da aka samu ibtila’i na garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ko kuma hare-haren yan ta’adda.
Galibi dai jihohin kudancin Najeriya na matsawa gwamnatin tarayya a duk sanda irin wannan lamari ya faru ta yadda take aikewa da manyan jami’an tsaro cikin gagagwa domin tabbatar da ganin an daƙile matsalar idan ta faru a yankin kudanci, amma a Arewacin kasar har kawo yanzu akwai daruruwan mutane da aka gaza ceto su daga hannun yan bindiga.
Kan haka wakilinmu Ƙaribullah Abdulhamid Namadobi ya tattauna da Kyaftin Abdullahi Bakoji Mai-Ritaya kan ko me ya kawo wannan banbanci?
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...