
About
A wannan rana, ta biyu ga watan Afrilun shekarar 2026 da muke, wa’adin shugabancin hamɓararen shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar Muhammad Bazoum ke ƙarƙarewa da a ce yana kan karagar mulki. A irin wannan ranar ce dai ta watan Afrilun shekarar 2021, aka rantsar da Mohammed Bazoum a matsayin shugaban Jamhuriyar Nijar, bayan da ya lashe sama da kashi 55 na ƙuri’un zaɓen da aka yi a watan Fabrairun wannan shekara.
Akan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Intinikar Alhassan, ɗaya daga cikin makusantan hamɓararren shugaban na Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu............