Skip to content
Opens in a new window
Ibrahim Salissou kan sauyin da aka samu a Nijar bayan juyin mulki
27 July 2026

Ibrahim Salissou kan sauyin da aka samu a Nijar bayan juyin mulki

Bakonmu a Yau

About

A jamhuriyar Nijar jiya lahadi aka cika shekaru 3 da kifar da Mohamed Bazoum daga kujerar shugancin ƙasar bayan ya share shekaru biyu da watanni uku kan karagar mulki.

Sojoji a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahman Tiani, babban kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ne suka sanar da kifar da gwmanatin.

Ibrahim Salissou shi ne shugaban ƙungiyar FRSA mai fafutukar ƴantar da Afirka, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal cewa tabbas an samu sauyi cikin shekaru ukun da suka gabata a ƙasar.

Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...