Ibrahim Bello Rigachikun akan hukuncin kotun ƙoli na ikon dakatar da gwamnoni
17 December 2025

Ibrahim Bello Rigachikun akan hukuncin kotun ƙoli na ikon dakatar da gwamnoni

Bakonmu a Yau

About

A farkon wannan Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar wa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ƙarfin ikon kafa dokoar ta ɓaci a kowace jiha da ke faɗin ƙasar, idan buƙatar hakan ta taso, domin tabbatar da zaman lafiya.

 

Yayin yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatocin jihohin da ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP suka shigar, Kotun ta ce shugaban ƙasa na da ikon dakatarwar wucin gadi ga zaɓaɓɓun shugabannin jihar da dokar ta ɓacin ta shafa.

Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Ibrahim Bello Rigachikun da ke Najeriya.