
About
Hukumar kwallon ƙafar Afrika ta sanar da ƙwace Kambun da Senegal ta lashe a gasar neman kofin nahiyar da aka kammala cikin watan Janairun da gabata tare da miƙa shi A a hannun ƙasar Moroko.
Wannan dai mataki ne da ya yi matuƙar girgizar masu shawar harkar ƙwallon ƙafa ba wai a nahiyar Afrika ba har da sauran sassan duniya. To sai tuni Senegal ta buƙaci a gudanar da bincike bisa zargin cewa akwai yiyuwar an bayar da rashawa ne don ƙwace wannan galaba.
A game da wannan mataki ne Michael Kuduson ya zanta da Aliyu Awwal Ibrahim, Sakataren tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ƴan ƙasa da shekaru 20. Ga kuma zantawarsu.
A latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar tattaunawar.