
15 July 2026
Hon Satomi kan yadda wani shingen jami'an tsaro ke haddasa asara rayuka a Borno
Bakonmu a Yau
About
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga rundunar sojin saman ƙasar da ta buɗe ɓangaren hanyar Maiduguri zuwa Kano da ta toshe a anguwar Ngomari-Pompomari da ke wajen birnin Maiduguri kusan shekaru 10 wanda ke haddasa asarar ɗumbin rayuka.
Ɗan Majalisa mai wakiltar Jere a jihar Borno, Hon. Satomi da ya gabatar da ƙudirin gaban Majalisar a makon jiya, ya yi wa Ahmed Abba ƙarin bayani dangane da girman matsalar da toshe hanyar ya haifar da kuma ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ceto ɗalibai da malamai da Boko Haram ta yi garkuwa da su a Askira-Uba na jihar Borno.
Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.