Hon Sani Ahmed Toro kan ƙalubalen samun takardar Visa zuwa gasar lashe kofin duniya
02 June 2026

Hon Sani Ahmed Toro kan ƙalubalen samun takardar Visa zuwa gasar lashe kofin duniya

Bakonmu a Yau

About

A yayin da ya yage kwana 9 a fara gasar lashe kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci, har yanzu wasu ƙasashe na ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen samun takardar izinin shiga ƙasashen. Ko a baya-bayan nan, anga yadda ƴan wasan tawagar ƙasar Afrika ta Kudu suka samu jinkiri wajen tafiya gasar sabida dalilai na Visa, bayaga ƙalubalen da ƙasashen Jamhuriyar Dimukaraɗiyyar Congo da Iran suma suka fuskanta.

Kan wannan batu Khamis Saleh ya tattauna da Hon Sani Ahmed Toro, tsohon sakataren Hukumar Kwallon Ƙafara ta Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu..........