Hon Sani Ahmad Toro kan yadda Najeriya ta gaza samun tikitin World Cup
18 November 2025

Hon Sani Ahmad Toro kan yadda Najeriya ta gaza samun tikitin World Cup

Bakonmu a Yau

About

Fatan Najeriya na samun gurbi a gasar cin kofin duniyar da za'a yi a shekara mai zuwa ya gushe, sakamakon rashin nasarar da ƙungiyar Super Eagles ta yi a hannun ƙasar Congo.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba zata je gasar ta dunitya ba, bayan gaza zuwa Qatar shekaru 4 da suka gabata, kafin wannan karo.

Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da tsohon sakatare janar na Hukumar Kwallon Kafa Najeriya, Hon Sani Ahmad Toro game da wannan koma baya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.