
14 November 2025
Hon Hamisu Mu'azu Shira kan dambarwar da ke tattare da babban taron jam'iyyar PDP
Bakonmu a Yau
About
Shugaban kwamitin shirya babban taron Jam'iyyar PDP na ƙasa a birnin Ibadan dake Najeriya, Umar Fintiri, wanda shi ne Gwamnan Adamawa, ya ce babu abinda zai hana su gudanar da taron da suka shirya gobe asabar.
Fintiri ya bayyana haka ne bayan wani gagarumin taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka gudanar yau a birnin Abuja.
Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Hamisu Mu’azu Shira, ɗaya daga cikin jiga jigan jam’iyyar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.