
About
Kimanin gwamnonin jihohin Najeriya 20 sun amince su gina katafariyar ruga ta zamani a jihohinsu wadda za ta kunshi makarantu da asibitoci da kasuwanni har ma da wuraren kiwon dabbobi musamman shanu da zummar zaunar da Fulani makiyaya wuri guda ba tare da gararanba ba.
Tuni masana suka ce wannan sabon tsarin zai yi tasiri wajen tabbatar da lafiyar dabbobin Najeriya tare da ruɓanya adadin madarar da suke samarwa a kullum.
Jim kaɗan da kammala taro kan wannan shiri a birnin Lagos, Abdurrahman Gambo ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara kan noma da kiwo.
Latsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...