08 October 2026
Engr Saad Abdullahi kan rashin sanya Arewa cikin aikin sabunta tashoshin jiragen ruwa a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
Yayin da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin sabunta tashoshin jiragen ruwan ƙasar domin inganta ayyukan su, wasu ƴan arewacin ƙasar na zargin cewar ba a yiwa yankin su adalci ba, wajen rashin sanya tashar jiragen ruwa ta Baro cikin aikin, wanda gwamnatin tarayya ce za ta biya. Engr Saad Abdullahi, tsohon jami'in kamfanin mai na ƙasar, wato NNPC ya bayyana damuwa a kan yadda ƴan majalisun arewa da kuma fitattun mutanen yankin suka kauda kai a kan lamarin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu............