Dr Yahuza Getso kan sabbin hare-hare ƴan bindiga a Arewacin Najeriya
20 November 2025

Dr Yahuza Getso kan sabbin hare-hare ƴan bindiga a Arewacin Najeriya

Bakonmu a Yau

About

Matsalolin tsaro na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Tarayyar Najeriya, bayan da a baya-bayan nan aka ga yadda ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar suka sace ɗalibai aƙalla 25 a jihar Kebbi, yayinda ana tsaka da jimamin wannan kuma aka sake ganin yadda suka kai hari wata majami’ar jihar Kwara tare da kashe mutane 2 da kuma sace wasu da dama.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan dakarun Sojin Najeriyar sun sanar da samun gagarumar nasara a kan ƴan ta’adda musamman bayan barazanar Trump ta ɗaukar matakin Soji kan ƙasar ta yammacin Afrika.

Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a Najeriyar Dr Yahuza Getso........