Dr. Yahuza Getso kan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai jihar Borno
09 March 2026

Dr. Yahuza Getso kan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai jihar Borno

Bakonmu a Yau

About

Rundunar sojin Najeriya ƙarkashin dakarun ‘Operation HADIN KAI’, ta musanta rahotanni da ke cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji 40, a wani mummunan hari da suka kai Jihar Barno. 

Sanarwar mai magana da yawun rundunar Lt. Col. Sani Uba, na zuwa ne, bayan da rahotanni suka ce, mayakan Boko Haram da aka tarwatsa su daga dajin Sambisa, suka sake haɗa kai tare da afkawa ƙauyukan Konduga da Ngoshe da Mainok da Jakana, inda bayanai suka ce sun kashe wani adadi mai yawa na sojoji da fararen hula a Ngoshe tare da sace da dama.

Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar Ahmed Abba da Dakta Yahuza Getso matsanin tsaro a Najeriya.........