Skip to content
Opens in a new window
Dr Umar Kwairanga kan kammala sayar da hannayen jarin matatar Dangote
29 October 2026

Dr Umar Kwairanga kan kammala sayar da hannayen jarin matatar Dangote

Bakonmu a Yau

About

Katafaren kamfanin Aliko Dangote ya sanar da cewar masu zuba jari daga ƙasashe 120 ne suka sayi hannayen jarin matatar sa da ke Lagos, wadda ta samu riɓi uku na kuɗaɗen da ta shirya samu a kasuwar hannayen jarin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce wasu majiyoyi na daban guda biyu da ke da masaniya kan cinikin hannayen jarin, sun ce matatar ta samu kuɗin da ta sarai za ta samu har sau uku, kuma naira triliyan 6 da biliyan ɗari 4 ko kuma dala biliyan 4 da miliyan ɗari 7 da 80 daga cikin Najeriya suka fito.

Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da DR Umar Kwairanga, shugaban hukumar hada hadar hannayen jarin Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai