Dr Mubarak Muhammad kan naɗin sabon firaministan Faransa Lecornu
11 September 2025

Dr Mubarak Muhammad kan naɗin sabon firaministan Faransa Lecornu

Bakonmu a Yau

About

Sabon firaministan Faransa Sebastien Lecornu ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin daga hannun Francois Bayrou, wanda ƴan Majalisar dokokin ƙasar suka tsige a ranar Litinin ta gabata.Wannan dai shi ne Firaminista na 5 bayan da Emmanuel Macron ya karɓi ragamar mulki domin yin wa’adi na biyu, lamarin da ke nuni da cewa ƙasar na fama da rikici a fagen siyasa.

Dr Mubarak Muhammad, mazauni Faransa kuma masani a game da salon siyasar ƙasar, ya bayyana wa Nura Ado Sulaiman mahangarsa a game da wannan batu.

Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu..................