Dr Kassum Garba Kurfi kan yarjejeniyar Ɗangote da kamfanonin dillancin Fetur
26 February 2026

Dr Kassum Garba Kurfi kan yarjejeniyar Ɗangote da kamfanonin dillancin Fetur

Bakonmu a Yau

About

A Najeriya, Matatar Man Dangote mafi girma a Afirka ta cimma matsaya da wasu manyan kamfanonin dallancin Mai guda 12 domin rarraba man fetir kimanin lita miliyan 60 zuwa 65 a kowace rana.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana haka cikin wata sanarwar, da ya ce gagarumin mataki ne na wadata kasar da mai da kuma dogaro da kai a bangaren makashi.

Domin sanin tasirin matakin, Ahmad Abba ya tattauna da Dr. Kasum Garba Kurfi, masanin tattalin arziki a Najeriya.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.