
About
Wata cibiya da ke bibiyar ayyukan Kamfanonin sojojin haya a sassan Duniya, ta ce kusan mutane dubu 1 da 500, Rasha ta ɗiba daga ƙasashen Afrika aƙalla 35, a matsayin sojojin haya a yaƙin da take gwabzawa da Ukraine.
Rahoton ya ƙara da cewar daga cikin jimillar ‘yan Afrikan da suka shigar wa Rasha yaƙin da take da Ukraine a tsakanin shekarar 2023 zuwa tsakiyar bara, 316 sun mutu.
Don jin irin kallon da masana tsaro ke yi wa lamarin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting mai binciken tsaro a nahiyar Afrika.
Latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawarsu ta gudana...