16 September 2026
Dr Kabiru Adamu kan ƙara yawan makaman da Najeriya ta sayo daga ƙetare
Bakonmu a Yau
About
Wani rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ya nuna cewar, yawan makaman da gwamnatin ƙasar ke sayowa daga ƙetare da zummar inganta tsaro a ƙasar ya ƙaru da kaso 104, inda ta kashe Naira biliyan 55 a cikin watanni shidda na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da abinda aka kashe wajen sayen makaman a shekarar bara.
Tuni dai masana da sauran ƴan Najeriya suka fara bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan rahoton, inda wasu ke yabawa, yayin da wasu ke ganin bai kamata a dogara da ƙasashen ƙetare wajen samar da makamai ba.
Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting mai binciken tsaro a nahiyar Afrika.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu.............