About
Ƙura ta lafa a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar bayan da wasu sojoji suka kai hari filin jirgin sama da fadar shugaban ƙasar, a wani bore da suka fara tun cikin daren Juma’a zuwa wayewar safiyar Asabar, lamarin da ya haifar da musayar wuta da fashe-fashe na tsawon sa'o'i. Rahotanni na cewa dakarun hayar Rasha sun taimaka wajen daƙile boren na ƙananan sojoji da suka kaucewa fagen daga domin farmakan babban birnin.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Ahmad Abba da Dr. Kabiru Adamu, masanin tsaro a yankin Sahel.......