
22 April 2026
Dr Auwal Aliyu kan yarjejeniyar shimfiɗa bututun Gas tsakanin Najeriya da Morocco
Bakonmu a Yau
About
Najeriya da Morocco sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar shimfiɗa bututun Gas, aikin da zai laƙume kuɗin da yawansu ya kai Dala biliyan 25, kafin ƙarshen wannan shekara. Bayanai sun ce tsawon bututun Gas ɗin da za’a shimfiɗa ya kai kilomita dubu 6,900, wanda zai ratsa cikin Ruwa da Sahara, har ma ya tsallaka zuwa Turai.
Kan wannan Shamsiyya Haruna ta tattauna da Dakta Abdullahi Auwal Aliyu, masanin tsaro a Najeriya, domin jin yiwuwar wannan aiki da kuma tasirin da zai yi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar ta su.................