17 November 2026
Dr Ahmed Bedu, kan alƙawarin Tinubu na kakkabe Boko Haram cikin shekaru 5
Bakonmu a Yau
About
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da shirin murƙushe ƙungiyar boko haram na shekaru biyar, muddin ƴan Najeriya suka sake zaɓen sa a shekara mai zuwa. Ministan ma'adinai kuma kakakin yaƙin neman zaɓen sa Dele Alake ya ce shugaban ya bada umarnin ɗaukar sojoji 28,000 da kuma ƴansanda 50,000. Alake ya ce sun yi nasarar hallaka sama da mayaƙa 15,000, yayin da wasu dubu 130,000 tare da iyalan su suka aje makaman su tare da miƙa kan su.
Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Ahmed Bedu, malami a jami'ar Maiduguri, kuma ɗan yankin, ga yadda zantawar su ta gudana a kai.