
22 December 2025
Dauda Iliya hadimin Gwamnan Borno kan ƙaddamar da motocin sauƙaƙa sufuri a jihar
Bakonmu a Yau
About
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinibu ya ƙaddamar da ababen hawa na sufuri masu amfani da lantarki guda dubu 3 da 620 da gwamnatin jihar Borno ta tanadar domin sauƙaƙa sufuri a tsakanin al’ummarta.
Motocin sun haɗa ne da Kekuna dubu 3 da babura masu ƙafa 3 ko kuma adaidaita sahu guda 500 sai kuma ƙanana da manyan Motocin safa ko kuma bas bas masu ɗaukar mutum 20 da 42 guda 100, kari ga wasu motoci 650 masu amfani da lantarki da gwamnati ta samar don sufuri.
Dangane da wanna ne Faruk Muhammad Yabo ya tattauna da Dauda Iliya mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Borno a fannin watsa labarai inda ya fara da tambayarsa yadda ababen hawan suke da kuma yawansu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...