Dakta Isa Abdullahi kan matakin CBN game da cire kudi a bankuna
04 December 2025

Dakta Isa Abdullahi kan matakin CBN game da cire kudi a bankuna

Bakonmu a Yau

About

Babban Bankin Najeriya ya sanar da cire shingen kuɗaɗen da jama'a ke ajiyewa a bankuna da kuma ƙara yawan kuɗin da ake ɗauka a bankin.

Bankin ya ce daga yanzu an ƙara yawan kuɗin da mutum ka iya cirewa daga naira 100,000 zuwa naira 500,000, yayin da bankin ya ci gaba da riƙe naira N100,000 a matsayin kuɗin da mutum guda ka iya cirewa a ATM a rana guda.

Domin duba tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi, na Jami'ar Kashere, da ke jihar Gombe a Najeriya.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.