
About
Wasu alƙaluma daga Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur na kan tudu da na cikin ruwa (NMDPRA) sun nuna cewa, adadin Iskar Gas ɗin da aka fitar daga Najeriya zuwa kasuwannin ƙetare ya kai kaso 62 cikin 100, cikin watanni uku na farkon wannan shekara.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gas ɗin ya yi ƙaranci a Najeriyar, lamarin da ke taka rawa wajen raguwar hasken lantarkin da ake samu, fannin da kasonsa aƙalla 80 cikin 100 ya dogara da arziƙin na Gas.
Don jin yadda masana ke kallon lamarin da kuma mafita, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau, ƙwararren kan tattalin arziki a Najeriya.
Latsa alamar sauti don sauraron hirar: