Dakta Abubakar Sadiq kan matakin rushe wasu jam'iyyu siyasa a Najeriya
16 June 2026

Dakta Abubakar Sadiq kan matakin rushe wasu jam'iyyu siyasa a Najeriya

Bakonmu a Yau

About

Wata babbar kotu a Najeriya, ta bai wa hukumar zaɓe ta INEC umarnin soke wasu jam'iyyun adawa har guda biyar, saboda saɓawa dokokin zaɓen shekarar 2023 na ƙasa samun kashi 25 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Jam'iyyun sun haɗa da ADC da AA da APP da ZLP da Acoord Party.

Tuni wannan hukunci ya haifar da mahawara da kuma zargin yunƙrin haa 'yan adawa shiga zaɓe mai zuwa.

Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Abubakar Sadiq Gombe, shugaban Jam'iyyar adawa ta SDP.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.