
About
A Najeriya ra’ayoyi sun sha bambam a tsakanin al’umma dangane da shirin bai wa jihohi damar kafa rundunar ƴansanda don inganta sha’anin tsaro a ƙasar.
Tuni dai Majalisun Tarayyar Ƙasar biyu suka amince da daftarin dokar da ke bayar da damar ɗaukar wannan mataki, kamar dai yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta buƙata.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon Kwamishinan Ƴansanda CP Muhammed Indabawa mai ritaya, domin jin yadda masana aikin ɗansanda ke kallon matakin.
Latsa alamar sauti don sauraren zantawarsu...