
19 February 2026
Barista Abubakar kan Kotun ECOWAS da ta koka da Najeriya game da hukunce-hukunce
Bakonmu a Yau
About
Kotun ECOWAS ta koka kan alƙaluman da suka nuna cewar cikin shekaru 25, wato tun bayan da ta fara aiki a shekarar 2001, hukunce-hukunce gud 10 kaɗai Najeriya ta mutunta, 66 da ta yanke.
Shugaban Kotun ta ECOWAS Ricardo Claudio ne ya bayyana alƙaluman yayin buɗe taron masu ruwa da tsaki da babbar ƙotun ƙungiyar ƙasashen ta Yammacin Afrika a Najeriya.
Domin jin yadda masana ke kallon lamarin, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Barista Abubakar Mujitafa Gagare, ƙwararren lauya da ke Najeriya.
Latsa alamar sauti don jin yadda tattaunawar ta gudana...