19 October 2026
Auwal Jibril kan shirin farfaɗo da kasuwanci tsaƙanin Najeriya da Faransa
Bakonmu a Yau
About
Yanzu haka wata tawagar Najeriya da ta ƙunshi jami’an gwamnati da kuma ƴan kasuwa, tana gudanar da ziyara a Faransa inda ta tattauna da mahukuntan ƙasar kan yadda za a haɓaka kasuwanci a tsakanin ƙasashen biyu.
Batun bayar da dama ga ƴan Najeriya domin shigar da kayan amfanin gona a Faransa, shi ne abu mafi muhimmanci da aka share kusan makon ɗaya ana tattaunawa a kai, kamar dai yadda ɗaya daga cikin ƴan kasuwar na Najeriya Alhaji Auwal Jibril, shugaban kamfanin Azuretti Services and Distribution da ke dillancin kayan amfanin gona daga Najeriya ya kasance a cikin tawagar, ga kuma ƙarin bayanin da ya yi wa Abdoulkarim Ibrahimn Shikal.