Ana sa ran samun fahimtar juna tsakanin Nijar da Benin
28 May 2026

Ana sa ran samun fahimtar juna tsakanin Nijar da Benin

Bakonmu a Yau

About

Bisa ga dukkan alamu za a iya samun fahintar juna tsakanin Nijar da kuma maƙociyarta Jamhuriyar Benin, waɗanda ke takun-saka tun bayan kifar da gwamanatin dimokuraɗiyyar ta Mohamed Bazoum yau kusan shekaru uku kenan.

Kasancewar Firaminsitan Nijar Mahamane Ali Lemine Zeine a wurin bikin rantsar da sabon shugaban Benin Romuald Wadagni, na ƙara nuni da cewa za a iya samun kusanci a tsakanin ɓangarorin  biyu.

A game da haka ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Adamu Muhammadu Ɗan Madawa, ɗaya daga cikin shugabannin ƴan Nijar mazauna Najeriya.

Latsa alamar sauti don sauraren zantawarsu...