11 September 2026
An naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
A Najeriya an naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙin da ake da ƙungiyoyin ta’addancin na ISWAP da Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ke nuni da cewa an maye gurbin wanda ke jagorantar wannan runduna ƙasa da shekaru biyu bayan naɗa shi kenan.
Shin wanan sauyi ya dace da halin da ake ciki na yaƙi da ta’addanci ko kuma dai kawai garambawul ne da aka saba yi? Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Detective Awwal Bala Durumin Iya masanin tsaro ne a Najeriya.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.