Amnesty ta zargi Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su
21 November 2025

Amnesty ta zargi Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su

Bakonmu a Yau

About

Ƙungiyar Amnesty International ta zargi hukumomin ƙasar Chadi da gazawa wajen ɗaukar matakan kare mutanen da ake cin zarafin su, sakamakon rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙasar, yayin da ta ce  tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, an kashe mutane 98, baya ga jikkata sama da 100 da kuma tilastawa ɗaruruwan iyalai barin muhallin su. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Isa Sanusi Daraktan kungiyar a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.