
Ƙungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta dauki matakai na gaggawa don kare dalibai da kuma ceto wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.
Ƙungiyar ta jaddada cewa gazawar hukumomi wajen kawo ƙarshen hare-hare da sace-sacen dalibai na nuna cewa rayuwar yara na cikin matsananciyar barazana.
Ƙungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki matakin gaggawa na kawo karshen satar yara da kai hari makarantu, tana mai cewa iyaye sun gaji da romon bakar da ake musu.
Amnesty ta zargi gwamnatin da kasa kare kananan hukumomi, musamman a jihar Zamfara da sauran yankunan Arewa daga hare-haren yan bindiga.
Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda tsadar rayuwa da matsalar tsaro ke raba iyalai da muhallansu, lamarin da ke jefa yara da dama cikin yunwa da rashin ilimi.
Kan wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan Ƙungiyar a Najeriya Isah Sunusi.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.