Ambasada Cika akan iƙirarin Trump na tattaaunawa da Iran
24 March 2026

Ambasada Cika akan iƙirarin Trump na tattaaunawa da Iran

Bakonmu a Yau

About

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba dan tattaunawar da gwamnatinsa ta yi da wani babban jami’in ƙasar Iran ba, to lalle da babu makawa ya ƙaddamar da farmaki domin rusa cibiyoyin samar da wutar lantarki na ƙasar.

Trump ya ce ya jinkirta kai farmaki har tsawon kwanaki biyar, tare da yiyuwar hakan ya kasance damar cimma yarjejeniya da Iran a cewarsa.

Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon jakadan Najeriya a Iran Ambasada Alhaji Abubakar Cika, domin jin tasa fahintar a game da dalilan jinkirta kai wannan hari. Ga kuma abin da yake cewa.