Alhassane Intchinicar kan sharuɗɗan da Nijar ta kafa kafin buɗe iyaka da Benin
22 June 2026

Alhassane Intchinicar kan sharuɗɗan da Nijar ta kafa kafin buɗe iyaka da Benin

Bakonmu a Yau

About

An fara tattaunawa tsakanin Benin da kuma Jamhuriyar Nijar da nufin sake buɗe iyakar ƙasashen biyu, sai dai mahukuntan birnin Yamai sun gindaya sharuɗɗa biyu kafin sake buɗe iyakar.

Ministan cikin gida kuma jagoran tawagar Nijar a tattaunawar, ya ce na farko dole ne a ƙulla yarjejeniyar tsaro wadda a ƙarƙashinta ba ɗaya daga cikin ƙasashen biyu da za ta bari a yi amfani da ita domin kai wa ɗaya hari, sai kuma a kafa wata cibiyar musayar bayanan sirri ta haɗi-gwiwa da za ta bai wa Nijar damar sa-ido a game da kai-da-kawon sojojin ƙetare a kusa da iyakarta da Benin.

Dangane da wannan Oumarou Sani ya tattaunawa da Alhassane Intchinicar guda daga cikin waɗanda suka jima suna fafutukar ganin a sake buɗe iyakar ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.