
08 September 2025
Alhaji Dayyabu Garga akan batun fara yajin aikin ƙungiyar NUPENG a Najeriya
Bakonmu a Yau
About
A wannan litinin, ƙungiyar NUPENG da ta haɗa direbobin motocin dakon mai da iskar gas a Najeriya ta fara yajin aiki, domin nuna rashin amincewa da yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motocinsa domin rarraba man fetur a sassan ƙasar.
Shugabannin NUPENG, sun ce su ne ke da hurumin raba mai da kuma iskar gaz a Najeriya, a maimakon yadda Ɗangote ke shirin yin amfani da motoci dubu huɗu domin wannan aiki.
Latsa alamar sauti domin sauraro.......