
17 June 2026
Akwai takaici yadda wasu ke son haddasa gaba tsakanin ƙabilu a Plateau-Joyce Ramnap
Bakonmu a Yau
About
Gwamnatin Jihar Filato da ke Najeriya ta bayyana matuƙar damuwar ta dangane da yadda ta ce wasu na amfani da hukuncin wata kotu dangane da baiwa wasu Hausawa takardar zama ƴan ƙasa domin haifar da tashin hankali a tsakanin al'ummar da suka kwashe shekaru da dama su na zaman lafiya da juna.
Gwamnatin ta ja kunnen al'umma inda ta ce waɗanda ba su gamsu da hukuncin ba na da hurumin ɗaukaka ƙara kamar yadda dokokin ƙasa da suka tanada.
Bashir Ibrahim Idris ya tuntuɓi kwamishiniyar yaɗa labaran jihar da ta gabatar da sanawar, Joyce Ramnap kuma ga yadda zantawarsu ta gudanar a kai.