
About
A jiya ne ake faro taron kwanaki biyu tsakanin Faransa da ƙasashen Afrika a birnin Nairobi, wanda shugaba Emmanuel Macron da takwaransa William Ruto ke jagoranta.
Taron ya haɗa shugabannin ƙasashen Afrika, da Hamshaƙan ƴan Kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan nemawa nahiyar Afrika mafita wajen samun ci gaban Tattalin Arziƙi a fannonin da suka haɗa da, bunƙasa Masana’antu da Kimiyya da Fasaha da inganta Noma da Tsarin Kiwon Lafiya, da kuma samun wadatar makamashi.
Danna alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar Nura Ado Suleiman da hadimin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Daniel Bwala.......