
About
Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure.
Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar.
Irin wannan bincike, ya taimaka matuka wajen tantance masu neman aure tare da dakile wadanda ke da matsaloli a fannin dabi’u, rashin halayen kwarai da kuma matsala a fannin lafiya.