
Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo?
Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar guza, sannan a ɗaura masa tsirkiya guda biyu ko uku.
A cikin shekarun da suka gabata, manyan mawaƙa irinsu Rabi'u mai Gurmi Gumel da Rabe mai Gurmi Jibia sun zagaya duniya suna baje kolin wannan fasaha.
Amma a yau, idan ka zagaya biranen ƙasar Hausa, da kyar kake jin sautin wannan kiɗa, maimakon haka, sautin kiɗan na’urorin zamani na matasa sune suka mamaye ko'ina.
Duk da wannan ƙalubale, wasu mawaƙan zamanin na ƙoƙarin haɗa sautin gurmi da kiɗan zamani don janyo hankalin matasa da kuma kaucewa ɓacewar wannan muhimmin kiɗa na al'ada.