Sharfadi Technology

Sharfadi Technology

12 episodes
Daga Shafukan Sadarwa shirin dake tattauna batutuwan da suka shafi shafukan internet da kuma rahotonni daga makarantunmu.

Sharfadi Technology

Sorted by
10 December 2019

Daga Shafukan Sadarwa 10-12-2019

Basheer Sharfadi
03 December 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 03-12-2019

Basheer Sharfadi

Shirin na Daga Shafukan Sadarwa shirin da ke kawo muku labarai da rahotonni kan kimiyya da fasahar zamani a kowane mako, shirin hadin gwiwa da cibiyar bincike da wayar da kan al’umma akan internet ta Sharfadi.com da kuma gidan Rediyon DITV Alheri Radio dake garin Kaduna.


Shirin na zuwa muku a duk ranar Talata da karfe 02:30 na rana sannan a maimata ranar Laraba da karfe 04:30 na yamma, a DITV Alheri Radio kan mita 97.7 a zangon FM a birnin Kaduna.

Haka kuma zaku iya sauraron wannan shiri dama sauran shirye-shiryen mu da suka gabata a koda yaushe kuke so daga ko ina a fadin duniya ta internet a www.sharfadi.com

Ga masu sha’awar tallata hajar su acikin shirin sai a tuntube mu ta lambobin waya kamar haka 0806480180, ko a 08142941884, ko kuma kai tsaye kuje sashen kasuwanci na gidan Rediyon DITV dake garin Kaduna.

https://www.podcasts.com/sharfadi-technology-9583ed302/episode/DAGA-SHAFUKAN-SADARWA-03-12-2019-16c7

31 October 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 31-10-2019

Basheer Sharfadi
14 September 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 14-09-2019

Basheer Sharfadi

Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi na biyu ya shawarci masu amfani da shafukan soshiyal midiya kan su maida hankali wajen kare mutunci da al’adar Mallam Bahaushe

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano tasha alwashin daukar matakin ba sani ba sabo akan masu aikata laifuka ta soshiyal midiya.

Sha’irai masu yabon Annabi (s.a.w) sun bayyana irin gudummuwar da shafukan social median ke basu wajen bunkasa al’amuransu. 

Wasu yara masu hazaka a Kaduna sun kera mota, da injin Markade da kuma Gadar Kawo.

Muna tafe da rahoto kan manhajar True Caller wadda ke baiwa mai amfani da ita damar bin diddigi kan lambar waya.

Zamu je Sokoto Inda wani matashi ya rungumi amfani da soshiyal midiyan ta hanyar bunkasa sana’arsa.

A can Zaria ma dai Malaman Addinin musulunci ne ke amfani da shafukan sada zumuntar wajen koyo da koyarwa.

Wadanda suka samu shiga shirin na wannan makon sune:

1. Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ||

2. DSP Abdullahi Haruna Kiyawa (Kakakin Rundunar 'Yansanda ta Jihar Kano).

3. Musa Garba Gashua MGG (Mai Waken Yabon Annabi (s.a.w).

4. Mallam Bello Hassan Almustapha (shugaban kungiyar Sokoto Development Society).

 5. Assidikul Akbar (Matashin da ya rungumi amfani da social media don bunkasa sana'arsa

6. Muhamamd Ibrahim Musa (Shugaban Kungiyar Yara Masu Hazaka ta Kaduna).

7. Engr Hussain (kwararran Injiniya a Kaduna).

8. Sheikh Abdullahi Jibrin (malamin addinin musulunci a Zaria).


SHIRYAWA:

1. Basheer Sharfadi

2. Idris M. Idris Damaturu

3. Safra'u Tijjani

4. Shamsiyya Abdullahi

5. Muslim Muhammad Yusuf

6. Sabi'u Dan Mudi

7. Aminu Dan Kaduna Amanawa

8. Muhammad Muhammad.

07 September 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 07-09-2019

Basheer Sharfadi

Sama da marasa lafiya 100 kungiyar tallafawa mabukata ta Fauziyya D. Sulaiman ta tallafawa da kudin magani ta hanyar Social Media

 

Kamfanin Opera ya bullo da wani sabon tsarin zirga-zirga da baburan adai-daita sahu ta hanyar amfani da wayar hannu a Kano

 

Wasu jama’a sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda manhajar tura kundin sakonnita Xender taso da sabon salo na hatimin tsaro wanda ake kira da bar code kafin tura sako, ko kun san meyasa aka kirkiro wannan sabon tsarin? Yaya sunan wanda ya kirkiro wannan manhaja?

 

An fara sayar da form ga dalibai masu sha’awar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano.

 

Muna tafe da rahoto kan yaduwar kalaman batanci a social media.

 

Zamu karkare shirin da sakonnin ra’ayoyinku, amma kafin nan bara mu leka sashen mu na talla.

01 September 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 31-08-2019 –SHAMSIYYA ABDULLAHI

Basheer Sharfadi

DAGA SHAFUKAN SADARWA 31-08-2019 –SHAMSIYYA ABDULLAHI

A yayinda akayi shagulgulan bikin ranar Hausa ta duniya, al’umma da dama sunyi amfani da ranar wajen bayyana maban-bantan ra’ayoyinsu ta shafukan sada zumunta.

Masana na ta yin fashin baki kan yunkurin gwamnatin tarayya na fara baiwa kafafan yada labarai na intanet lasisi.

Dara taci gida inji ‘yan Magana, wasu masu kutse sun sace asusun mutumin da ya kirkiri shafin Twitter

Hukumar binciken laifuka ta kasar Amurka ta cafke ‘yan Nigeria su 80 da laifin damfara ta yanar gizo.

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta kasa ta saki sakamakon jarrabawar dalibai na bana.

Wadanda suka samu shiga cikin shirin wannan makon:

1.     Abdulbaki Aliyu Jari -BBC Hausa (Matashin da ya kirkiri ranar Hausa).

2.     Malam Yusuf Ladan Sanyinna (Kwarrran malamin harshen Hausa)

3.     Zainab Nasir Ahmad (‘Yar gwagwarmayar Social Media).

4.     Engr. Jamilu Dahiru Ibrahim (Shugaban injiniyoyin Freedom Radio Group).

5.     Abdullatif Abubakar Jos (Jaridar SolaceBase).

Shiryawa:

Basheer Sharfadi

Idris M. Idris Damaturu

Safra’u Tijjani Adam

Shamsiyya Abdullahi

Muslim Yusuf Muhammad.

 

Ayi sauraro lafiya.

24 August 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 24-08-2019

Basheer Sharfadi

Hukumar HISBAH ta dakume wani matashi sakamakon hada hoton tsohuwar budurwarsa da yayi dana tsiraici ya kuma wallafa a shafin Facebook da sunan Itace

A yayinda hukumar Hisbar ke cewa ta baza idanuwanta a kowane ANGEL don cafke ‘yan daudu ta inda basa tsammani tuni wasu matasa sukayi amfani da shafin Facebook tun daga garin Kaduna, suka kulla alaka zuwa Kano domin aikata dabi’ar mutanen Annabi Ludu akan kudi N6,000 kacal.

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD ta bada horo ga wasu matasa kan yaki da kalaman batanci a Internet.

Muna tafe da jerin rahotonninmu na wannan makon, dama cigaban tattaunawarmu da matashin nan da ya kirkiri babbar kasuwarnan ta Internet wato GetkKano.

10 August 2019

DAGA SHAFUKAN SADARWA 10-08-2019

Basheer Sharfadi

Wani rahoto da kamfanin Facebook ya fitar ya nuna cewa ‘yan Nigeria ne kan gaba wajen tattauna batutuwan da suka shafin gasar cin kofin Africa data gabta, shin ko me hakan yake nufi?

Jami’an tsaro sun cafke wasu mutane biyu dake amfani da sunan mataimakin shugaban kasa, da kuma mai dakin shugaban kasar a Facebook

Dubun wani matashi ta cika bayan da shima ya bude asusun Facebook da sunan dan Sarkin Kano

Haka kuma muna tafe da rahoto kan yaduwar labaran karya da kuma kalman batanci a shafukan sada zumunta.

Kamar ko wane mako muna tafe da tattaunawa da wani matashi daga Kano ya kirkiri kasuwar internet.