About
Ku kasance tare da mu a sabon shirinmu na GWANI PODCAST, shiri na musamman da zai riƙa kawo muku fitattun malaman Alƙur’ani da manyan ƙwararru a fannin ilimin Alƙur’ani daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka.
Za mu riƙa tattaunawa da su, domin jin tarihin rayuwarsu, gudummawar da suke bayar a wajen hidimar Alƙur’ani, da irin nasarorin da suka samu a wannan fage, tare da mai gabatarwa: Dr. Abdurrazaq Kabir Hizqeel Makarfi.