Opens in a new window
53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA
05 July 2026

53 | YAƘI KO SULHU? MAKOMAR RIKICIN IRAN, AMURKA DA ISRA'ILA | DR. RAYA'UDDEEN ZUBAIR MAITAMA

ADPlusHausa | Podcast

About

Shin ana iya warware wannan rikici ta hanyar yaƙi, ko kuwa mafita tana cikin tattaunawa da diflomasiyya?

-------------------------------------A yau duniya na ci gaba da sa ido kan rikicin da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila. Tashin hankali na ƙaruwa, hare-hare na ci gaba, yayin da duniya ke tambayar kanta: Shin wannan rikici zai tsaya a nan, ko kuwa zai rikide zuwa babban yaƙin yanki? Mene ne mafita? Kuma wane tasiri wannan rikici zai iya yi ga tattalin arzikin duniya, tsaron ƙasashe, har ma da rayuwar al'ummar Afirka?

A wannan shirin na Rumfar Africa Podcast Hausa, za mu yi nazari cikin natsuwa tare da baƙo na musamman domin fahimtar tushen rikicin, matsayinsa a siyasar duniya, da hanyoyin da za su iya kai ga zaman lafiya.