DF Online Radio
Ga me da DF Online Radio
Wannan tasha, an samar da ita da nufin inganta fahimtar al’amuran Fasaha da Kimiyya ga al’umar Hausawa, musamman Dalibai masu nazari a wadannan fannoni da kuma sauran Jama’a masu ta’ammali da Na’urorin Zamani da sauran al’aumara masu alaka da wadannan.
Idan muka duba za muga cewa a kwai kasashe masu yawa da suka shahara a fannoni daban daban, musamman kere-kere da kirkire-kirkire wadanda kullum sai karuwa sukeyi a fadin Duniya. Wadancan kasashe da yawan su suna amfani da harsunan kasashen su ba turanci ba. Hakan ya basu babbar nasara wajan samun kyakkyawar fahimtar ilim kimiyya da fasahar da har takai su ga kasancewa a dukkan matsayin da suke kai a Duniya.
Sannan kuma akwai kalmomi masu yawan gaske a wadannan fannoni da ake haduwa dasu a wajan karantar su, wadanda fahimtar su na taka muhimmiyar rawa wajan inganta fahimta a lokacin nazari ko bincike. Wadannan kalmomi a dunkule ana kiran su a turance da Terminology. Kusan kowanne fannin Ilimi yanada irin nasa. Idan aka fahimce su, za’a sami kyakkyawar fahimta sosai. Saboda kalmomi ne da suke kunshe da gundarin ma’ana a darussan da suka bayyana a ciki. Idan har ba’a sami fahimtar su yadda ya kamata ba, hakika za’a sami rauni wajan aiki ko mu’amala a fannonin ilimi da yawa.
Kuma wannan shafi ba gwani ba ne, sai dai tsananin kishin harshen Hausa da neman tarayya da masana domin a gudu tare a tsira tare.